Babban Mai Magani
1. Babban mai magani ‘na nan,
Yesu mai jin tausayinmu.
Mu je mu nemi warkewa
A wurin Almasihu.
Korus
Yesu! suna mai daɗin ji,
Ba mai kamarsa, ba mai fi.
Ina sonsa kamar me !
Yesu Almasihu.
2. Mai ba da lafiya ne shi,
Cuta fa zunubanmu.
Mu je mu roƙi gafara
A wurin Almasihu.
3. Mai kawo gafara ne shi,
Ya ɗauke zunubanmu,
Ya kai su bisa itacen
A cikin jiki nasa.
4. Nan gaba za mu yabe shi,
Mun komo lafiyayyu.
Ba magani na zunubi
Sai wurin Almasihu.
5. Amma da dangi masu yawa
Da ba su da cetonsa,
Mu sai mu je mu neme su,
Mu kai su wurin Yesu.